Kasashen Turai za su rufe iyakokinsu saboda Coronavirus
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa, kasar ta shiga yanayi na yaki sakamakon cutar Coronavirus da ke ci gaba da lakume rayukan al’ummar kasar. A yayin jawabin da ya yi wa al’ummar kasar, shugaban ya ce kasashen Turai za su rufe iyakokinsu na kwanaki 30 domin shawo kan cutar.
Wallafawa ranar:
A jawabin da shugaba Macron ya yi na mintuna 20 ya ce, za su taikata zirga-zirgar jama’a na kwanaki 15 da kuma takaita mu’amalar jama’a kuma duk wanda aka samu ya karya dokar zai fuskanci hukunci.
Kuna iya alamar sautin da ke kasa domin sauraren bayanin Macron:
Jawabin shugaba Macron kan Coronavirus
Shugaba Macron ya ce, Faransa ta fada cikin yanayin yaki dangane da wannan cuta.
Macron ya kuma sanar da dage zaben 'yan majalisu da magadan-garin da aka shirya gudanarwa a karshen wannan mako.
Shugaban ya bukaci hadin kan al’ummar kasar wajen ganin an samu nasarar matakan da aka dauka, yayin da gwamnati za ta taimaka da kudade ga masu kamfanoni da sana’oi da wannan matsala ta shafa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu