Coronavirus

Halin da duniya ke cikin kan cutar Coronavirus

Mutana na rufe baki da hanci don kauce wa kamuwa da cutar Coronavirus
Mutana na rufe baki da hanci don kauce wa kamuwa da cutar Coronavirus REUTERS/Johannes P. Christo

Kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane dubu 7 da 63 sakamakon cutar Coronavirus wadda ta karade kasashen duniya 145, yayin da ta harbi jumullar mutane dubu 180 da 90.

Talla

Iran ta sanar a yau Talata cewa, wasu karin mutane 135 sun rasa rayukansu a sanadiyar Coronavirus, abin da ya sa alkaluman mamatanta suka kai 988.

Kasar Spain ta tabbatar da mutane kusan dubu 2 da cutar ta harba a yau Talata duk da matakan dakatar da al’amura da kasar ta dauka da suka hada da umarnin da ta bai wa al’ummarta miliyan 46 da su zauna a gida .

Kasar Brazil ta tabbatar da mutun na farko da Coronavirus ta hallaka a Sao Paulo wanda rahotanni suka ce, ya kai shekaru 62 da haihuwa.

Ita kuwa gwamnatin Poland ta killace wasu manyan jami’anta da suka hada da Firaminista bayan gwaji ya nuna cewa, wani Minista ya kamu da Coronavirus, yayin da mahukuntan kasar suka bullo da matakan gaggawa don yaki da cutar.

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya soke tarukansa da ya shirya gudanarwa a wannan mako duk dai saboda wannan cuta ta Coronavirus.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, akwai bukatar kasashen Turai su dauki tsauraran matakan yaki da wannan annuba a nahiyar wadda ta bayyaa a matsayin cibiyar cutar a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI