Coronavirus ta hana dalibai sama da miliyan 850 zuwa makaranta

Wasu dalibai sanye da kellen rufe hanci da baki don kariya daga kamawa da cutar coronavirus
Wasu dalibai sanye da kellen rufe hanci da baki don kariya daga kamawa da cutar coronavirus REUTERS

Hukumar Kula da Ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO tace yanzu haka dalibai sama da miliyan 850 basa zuwa makaranta a kasashen duniya sakamakon illar cutar coronavirus.

Talla

Hukumar wadda ta bayyana matsalar a matsayin babbar kalubale tace kasashe 102 suka sanar da rufe makarantun kanana da jami’oi, yayin da kasashe 11 suka rufe na wucin gadi.

UNESCO tace wannan adadi yayi daidai da rabin yawan daliban da ake da shi a fadin duniya, kuma yanzu haka tana tintibar ministocin ilimin kasashe akai akai domin samo hanyar dakile matsalar, yayin da wasu kasashe ke amfani da hanyar talabijin da rediyo wajen koyar da daliban su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.