Hannayen Jari da danyen mai sun fadi warwas

Wasu takardar kudin kasashen ketare
Wasu takardar kudin kasashen ketare STR / AFP

Masu ruwa da tsaki kan tattalin arziki, sun ce matakan rigakafin da gwamnatoci da kuma hukumomin duniya ke dauka sun gaza hana durkushewar kasuwannin hannayen jari na duniya gami da kasuwar danyen man fetur, saboda tasirin annobar Coronavirus da ta addabi duniya.

Talla

Rahotanni daga nahiyar Turai sun ce da safiyar yau laraba, kasuwannin hannayen jarin biranen, Frankfurt, London da kuma Paris da suke kasashen Jamus, Birtaniya da kuma Faransa sun tafka hasarar kashi 5 cikin dari, haka kuma abin yake ga kasuwannin hannayen jarin dake nahiyar Asiya.

A bangaren man faetur kuwa, yanzu haka farashin gangar danyen man ya yi mummunar faduwa irinta ta farko cikin shekaru akalla 17, bayan komawa dala 25 kan kowace ganga daga dala kusan 60 a baya, saboda tasirin annobar murar Coronavirus da ta tilasatawa kasashe dakatar da huldar kasuwanci ko zirga-zirga tsakaninsu.

A fannin canjin kudi kuma, dalar amurka ta kara daraja kan takwarorinta na duniya, ciki har da kudin yen na Japan da ake yiwa kallon wanda ke iya jurewa fuskantar matsalar tattalin arziki ko koma bayan da kan shafi duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.