Sanya safar hannu da rufe hanci baya hana yaduwar Coronavirus - Masana
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yayin da kasashen duniya suka dukufa wajen daukar matakan kariya daga yaduwar cutar coronavirus, kwararru sun yi gargadin cewa kyallayen da ake amfani da su don rufe baki da hanci da kuma safar hannu ba sa hana yaduwar cutar ga mafi yawan jama’a.
Masanan sun ce abin da ya fi dacewa shi ne, yawaita wanke hannaye, daina taba fuska, da kuma nisantar da juna.
Kasashe dai na kan daukar matakai daban-daban kan wannan cutar, inda tuni aka fara aiwatar da shirin zaman gida a kasar Faransa kamar yadda shugaba Emmanuel Macron ya bada umurni.
Domin sanin halin da ake ciki a nahiyar Turan sashin Hausa ya tuntubi Alhaji Sirajo Labo, Sarkin Hausawan Turai, mazaunin birnin Paris wanda ya shaida mana cewar alkawarin gwamnatin Faransa na tallafawa masana’atu da ma’aikata da kudade, ba zai hana matsalar da annobar ta haifar yin tasiri kan tattalin arzikin kasar ba.
Sarkin Hausawan Turai Alhaji Sirajo Labo
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu