Coronavirus-Duniya

Adadin mutanen da Coronavirus ke halakawa na dada hauhawa

Yawan mutanen da annobar murar Coronavirus ta kashe a sassan duniya ya haura dubu 9.
Yawan mutanen da annobar murar Coronavirus ta kashe a sassan duniya ya haura dubu 9. AFP / Joseph Prezioso

Hukumomin lafiya sun ce yawan mutanen da annobar murar Coronavirus ta kashe jimlace a sassan duniya ya haura dubu 9, gami da shafar wasu sama da dubu 210.

Talla

A gefe guda kuma alkalumman hukumomin lafiyar sun nuna cewar har yanzu annobar tafi barna a Italiya da kuma kasar Iran.

Alkalumman da hukumomin lafiyar suka fitar a yau sun bayyana cewar wannan annoba ta Coronavirus ta halaka jimillar mutane dubu 9 da 20, gami da shafar wasu dubu 217,510 bayan kutsawa cikin kasashe da manyan yankuna 157.

Rahotanni sun ce a jiya laraba kadai mutane 236 suka rasa rayukansu a sassan duniya dalilin cutar, yayinda ta kama wasu dubu 8 da 15.

A China inda cutar ta soma bulla, hukumomin lafiya sun yi nasarar dakile kaifin annobar, la’akari da cewar a jiya laraba karin mutane 34 kawai suka kamu da cutar, takwas kuma suka mutu.

Sai a kasar Iran, inda annobar ta Coronavirus ta fi barna, mutane 149 suka mutu a yau Alhamis kadai, wasu dubu 1 da 46 kuma suka kamu, abinda ya sanya jimillar wadanda cutar ta halaka a kasar kaiwa dubu 1 da 284, ta kuma shafi dubu 18 da 407 a jimlace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.