Coronavirus-Interpol

Bata gari na fakewa da Coronavirus wajen cutar jama’a - Interpol

Wasu likitocin kasar Switzerland a cibiyar binciken magunguna ta kasar dake Domat/Ems. 18/3/2020..
Wasu likitocin kasar Switzerland a cibiyar binciken magunguna ta kasar dake Domat/Ems. 18/3/2020.. REUTERS/Arnd Wiegmann

Rundunar ‘Yan Sandan duniya ta Interpol tayi gargadin cewar wasu bata gari na amfani da annobar coronavirus wajen cutar jama’a wajen basu kayayyakin kula da lafiya marasa inganci.

Talla

Rundunar tace yanzu haka ta kama mutane 121 da kuam kwace irin wadannan kaya mara sa inganci da kudin su ya kai Dala miliyan 14.

Cikin kayan da rundunar ta kwace a samamen da ta kai a kasashe 90 sun hada da kyallen rufe fuska marasa inganci da sinadarin da ake amfani da shi wajen tsaftace hannu da kuma wani magani da aka hana amfani da shi.

Rundunar tace ta gano shafunan intane 2,000 da ake tallata irin wadannan kayayyakin kula da lafiya da ake afani da su wajen kare kai daga cutar coronavirus, kuma ta kwace sama da 34,000.

Sakatare Janar na Rundunar Juergen Stock yace cinikin wadanann kayayyki ya nuna yadda wasu mutane basu damu da kare lafiyar jama’a ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.