Coronavirus

Miliyoyin mutane na gab da rasa ayyukansu saboda Coronavirus

Hukumar Kwadago ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, mutane sama da miliyan 25 za su rasa ayyukansu da suke cin abinci da su sakamakon bazuwar cutar Covid-19 da aka fi sani da Coronavirus.

Wasu ma'aikata da ke shirin zuwa wuraren aiki
Wasu ma'aikata da ke shirin zuwa wuraren aiki Reuters/Charles Platiau
Talla

A cewar Hukumar Kwadagon ta Duniya, akwai fargabar tarzoma da matsalolin tattalin arziki saboda yaduwar cutar wadda ta riga ta kashe mutane sama da dubu 8 a sassan duniya.

Guy Ryder, shugaban Hukumar Kwadagon ya ce, a yanzu annubar ba wai kawai bangaren kiwon lafiya ta shafa ba hatta bangaren harkan tattalin arziki da kuma ayyukan kwadago.

Hukumar na ganin cewa, dole ne duniya ta mike tsaye don tunkarar wannan babbar matsala da za ta shafi rashin ayyukan yi da dimbin jama'a ke cin abinci.

Kididdigar da Hukumar ta fitar ta nuna cewa, kimanin mutane miliyan 25 za su shiga sahun 'yan zaman kashe-wando, baya ga mutane miliyan 188 da aka yi rajistar su a matsayin marasa ayyukan yi a shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI