Coronavirus

Miliyoyin rayuka na gaf da salwanta idan ba a dauki mataki ba - Guterres

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Tiksa Negeri

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana fargabar cewar miliyoyin mutane na iya rasa rayukansu muddin aka bar cutar coronavirus ta ratsa kasashe matalauta, inda ya bukaci taimakon kasashen duniya wajen ganin an magance ta.

Talla

Yayin da yake tsokaci kan yadda cutar ke yaduwa a kasashen duniya, Guterres yace muddin aka gaza wajen dakile ta har ta shiga kasashen matalauta cutar zata kashe miliyoyin jama’a.

Sakataren yace hadin kan kasashen duniya ba wai ya zama wajibi bane, sai dai ya zama dole domin biyan bukatun kai.

Guterres yace lokaci yayi da kowacce kasa zata ce za tayi gaban kan ta wajen shawo kan cutar, inda yake cewa ya dace kasashen duniya su hada kan su wajen bayyanawa juna mataakn da suke sauka domin samun nasara.

Sakataren ya bukaci kungiyar kasashe masu arzikin masana’antu ta G-20 da su taimaka da arzikin da suke da shi wajen taimakawa kasashen dake Afirka ta Yamma da kuma wasu kasashe marasa karfi.

Guterres yace muddin wadannan kasashe suka ki taimakawa duniya zata gamu da bala’in da ba’a taba gani ba, sakamakon mutuwar miliyoyin jama’a wanda babu makawa a ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.