Amurka

Amurka ta daina bayar da biza

shugaban Amurka Donald Trump.
shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Leah Millis

Amurka ta  dakatar da bada biza a daukacin ofisoshinta da ke kasashen duniya saboda yaduwar cutar Coronavirus wadda yanzu haka ta kashe mutane sama da 10,000.

Talla

Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar da ta sanar da daukar matakin, ta kuma ce za a bar kofa a bude domin kula da bukatun gaggawa a ofishosihin jakadancin.

Amurka na daga cikin kasashen da cutar Coronavirus ta yi wa illa yanzu haka, inda aka killace miliyoyin mutane a gidajensu da kuma hana masu yawan shekaru fita ko ina.

A jawabin da ya yi wa Amurka a ranar Alhamis, shugaba Donald Trump ya zargi kasar China da rufa-rufa kan cutar wadda ta samo asali daga kasar, inda ya bai wa al’ummar kasar shawarar amfani da maganin zazzabin cizon sauro na chloroquine da hydroxychloroquine a matsayin riga-kafin cutar.

Trump ya ce, za su samar wa Amurka maganin cikin gaggawa domin amfani da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.