Lafiya

Coronavirus ta halaka rayuka kusan dubu 10

Wani likita a asibitin musamman na kula da masu cutar murar Coronavirus dake garin Cremona a kasar Italiya. 19/3/2020.
Wani likita a asibitin musamman na kula da masu cutar murar Coronavirus dake garin Cremona a kasar Italiya. 19/3/2020. REUTERS/Flavio Lo Scalzo

Sabbin alkalumman hukumomin lafiya sun nuna cewar jimillar yawan mutanen da annobar murar Coronavirus ta halaka a sassan duniya ya kai dubu 9 da 800.

Talla

A kasar Italiya kadai jimillar rayukan mutane dubu 3 da 400 suka salwanta tun bayan bullar annobar a kasar, da hukumar lafiya ta duniya tace a yanzu itace sabuwar cibiyar annobar, bayan China da ta yi nasarar dakile kaifinta.

Yanzu haka dai an fi samun yawan hasarar rayuka dalilin cutar a Italiya fiye da kasar China.

Tuni dai kasashe da hukumomin lafiya na duniya suka zafafa yaki da annobar ta Coronavirus yayin da yawan wadanda ke mutuwa ke ci gaba da karuwa a nahiyar Turai, duk da alamun sauki da aka samu a China, inda ba a samu wanda ya harbu da cutar ba a jiya alhamis.

Rahotanni sun ce yawan mutane da suka mutu a Spain ya karu har ninki 3 a cikin kwana guda, yayinda Italiya da Faransa suka shirya tsaf don ci gaba da killace miliyoyin mutane a gidajensu.

Kasashe a sauran sassan duniya sun garkame iyakokinsu, suka kuma tsaurara matakan tsaro, kana suka saki kusan dala tiriliyan daya a tsakaninsu don tallafawa tattalin arziki da ke durkushewa, amma kuma duk da haka cutar sai ci gaba da ta’azara take yi.

Alamun wannan cuta ta coronavirus dai sun hada da tari gami da zazzabi mai zafi, kuma adadin mutanen dake mutuwa na ci gaba da karuwa, haka ma wadanda suke harbuwa da cutar.

Wani mahimmin ci gaba da aka samu a kokarin da ake na dakile cutar shi ne, an samu ranar da ko da mutum guda bai kamu da wannan cuta a China ba, wato alhamis 19 ga watan maris da muke ciki, a karon farko tun bayan bullar cutar a birnin Wuhan na kasar.

A ranar alhamis din ce dai Kwararru kan sha’anin lafiya suka amince da soma yin amfani da Chloroquine da a baya ake amfani dashi kan zazzabin malaria, a matsayin maganin cutar ta Coronavirus da ta zamewa duniya annoba.

Cikin jawabinsa ga manema labarai a jiya alhamis, shugaban Amurka Donald Trump yace kwararrun dake karkashin hukumar kula da abinci da magunguna ta kasar sun bada tabbacin cimma matsaya kan shawarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI