Coronavirus ta tilastawa kusan mutane biliyan 1 zaman gida

Yadda birnin Paris ya zama fili sakamakon annobar Coronavirus da ta tilastawa jama'a zaman dirshan a gida.
Yadda birnin Paris ya zama fili sakamakon annobar Coronavirus da ta tilastawa jama'a zaman dirshan a gida. REUTERS/Gonzalo Fuentes

Akalla mutane biliyan guda ne a kasashen duniya aka tilastawa zama cikin gidajen su domin dakile cutar coronavirus wadda ta kashe mutane sama da 11,000 bayan ta ratsa kasashe sama da 160.

Talla

Alkaluman da aka tattara sun nuna cewar a cikin kasashe 35 kawai an killace mutane miliyan 900 a cikin gidajen su, cikin su harda miliyan 600 da gwamnatocin su suka hana fita baki daya.

Yayin da cutar tafi illa akan masu yawan shekarun da suka haura 60, shugaban hukumar kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya Tedros Adhanom Gebreyesus yace ya shaidawa matasa da cewar su yi taka tsan tsan domin cutar na iya kwantar da su a asibiti na makwanni ko ma hallaka su baki daya.

Ya zuwa yanzu cutar tafi illa a kasar Italia, inda ta kashe mutane 4,032, sai China inda ta kashe mutane 3,225, yayin da Iran ke matsayi na 3 saboda mutuwar mutane 1,556.

Kasar Spain ke matsayi na 4 da mutuwar mutane 1,002, sai Faransa mai 450, sannan Amurka mai 260.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.