Falasdinawa

Annobar Coronavirus ta shiga yankin Falasdinawa

Wasu jami'an lafiya yayin aikin tsaftace babbar kasuwar yankin Gaza don dakile yaduwar annobar murar coronavirus.
Wasu jami'an lafiya yayin aikin tsaftace babbar kasuwar yankin Gaza don dakile yaduwar annobar murar coronavirus. AP

A karon farko, yau lahadi hukumomin Falasdinawa a yankin Gaza, sun sanar da gano mutane 2 da suka kamu da cutar Coronavirus.

Talla

Dukkanin wadanda suka kamun Falasdinawa ne da suka dawo daga balaguron da suka yi zuwa kasar Pakistan, tuni kuma aka killace su.

A baya bayan nan ne dai majalisar dinkin duniya tayi gargadin cewar, barkewar annobar murar Coronavirus a yankijn Falasdinawa, ba zai yi kyawu ba, la’akari da rashin kyakkyawan tsarin kulawa da lafiya, da kuma talaucin da yay yiwa yankin katutu.

Tun a shekarar 2007 yankin na Falasdinawa ya soma fuskantar kuncin matsi na tattalin arziki, bayan takunkuman da Isra'ila ta kakaba masa, gami da tsaurara matakan tsaro kan iyakokinsu, da nufin dakile duk wani taimakon makamai da mayakan gwagwarmayar Falasdinawan ka iya samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI