Coronavirus

Annobar mura ta halaka sama da mutane dubu 13 a sassan duniya

Kusan mutane biliyan 1 ya tabbata an tilastawa zama a gidajensu daga jiya asabar zuwa yau lahadi, bayan karuwar adadin wadanda annobar murar Coronavirus ta halaka zuwa sama da dubu 13.

Adadin wadanda annobar Coronavirus ta halaka a Faransa ya kai 562.
Adadin wadanda annobar Coronavirus ta halaka a Faransa ya kai 562. Reuters
Talla

Yanzu haka dai cutar ta tilastawa kasashe 35 daga cikin sama da 150 da ta kutsa killace jama’a, abinda ya haifar da cikas ga sha’anin sufuri, kasuwanci da sauran lamuran yau da kullum.

Yanzu haka dai jimillar mutane dubu 300 aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar murar a sassan duniya.

A Italiya inda annobar ta muni, gwamnati ta rufe ilahirin masana’antun dake kasar bayanda cutar ta halaka mata kusan mutane 800 a rana guda, mafi munin hasarar rayuka tun bayan bullar cutar daga China wadda a yanzu ta yi nasarar dakile kaifinta.

A bangaren wadan suka kamu da cutar kuma a jiya asabar kadai, adadin ya kai dubu 6 da 557 a Italiyan, abinda ya kai jimillar yawan wadanda annobar ta shafa a kasar zuwa dubu 53 da 578.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI