Shugabannin addinai sun hada kai wajen daukar matakin dakile coronavirus

Malaman addinin Musulunchi da na  Kirista da kuma Yahudanci a Gabas ta Tsakiya sun hada kan su waje guda wajen daukar matakan rufe wuraren ibada domin dakile yaduwar cutar coronavirus dake cigaba da hallaka dimbin rayuka a duniya.

Adadin wadanda suka kamu d cutar yaa zarce dubu 13 AFP / Joseph Prezioso
Adadin wadanda suka kamu d cutar yaa zarce dubu 13 AFP / Joseph Prezioso AFP / Joseph Prezioso
Talla

Manyan malaman addinin Islama daga Saudi Arabia zuwa Masar da Iran tare da sauran kasashen Larabawa sun bada umurinin rufe Masallatai tare da hana taruwar jama’a domin kaucewa yada cutar.

A Birnin Kudus inda mujami’ar Latin take, inda ake bayyana ta a matsayin mafi tsarki, limamin ta ya bukaci mabiyan sa da su zauna cikin gidajen su wajen yin addu’oi.

Shugaban mabiya Yahudanci Yitzhak Yosef ya bada umurni ga mabiyan sa da su yi amfani da wayar su ta salula wajen samun bayanai dangane da cutar coronavirus lokacin da suke zaune a gidajen su.

Wannan ya nuna yadda manyan malamai a kasashen larabawa suka amince da kimar kimiya wajen goyan bayan shawarwarin da ake bayarwa dangane yakar cutar wajen kaucewa taron jama’a da kuma gudanar da ibada a gidaje.

Kasashen dake Yankin tekun Fasha da suka hada Saudi Arabia da Daular Larabawa da Kuwait da Qatar da Oman da Bahrain duk sun hana gudanar da sallar jam’i a Masallatai, kamar yadda kasashen Masar da Tunisia da Algeria dake Afirka suka yi.

Ita ma kasar Iran ta rufe manyan wuraren ibadar ta guda 4 ganin cewar itace kasar Musulmin da tafi fuskantar bala’in wannan cuta, yayin da shugaban addinin ta Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana goyan bayan sa ga matakan da masana kiwon lafiya ke dauka.

A kasar Lebanon mujami’u sun dauki matakan amfani da kafofin sada zumunta wajen yada addu’oi, yayin da Israila ta haramta duk wani taron mutane da ya wuce 10, abinda ya hana mabiya addinin Yahudanci taruwa domin gudanar da ibadar su ta minyan.

Wannan bai hana samun wasu malamai masu bada fatawar da ta saba da wannan ba domin halartar taruka ko wuraren ibadu.

Yayin da Ayatollah Ali Sistani ya bukaci mutane da su daina taruwa da yawa wajen ibada, daruruwan mutane sun yi gangami jiya asabar wajen tunawa da wani fitaccen malami Musa al-Kadhim wanda ya rasu a shekarar 799 lokacin da Khalifa Harun al-Rashid na Abbassid ya tsare shi.

Matakin ya biyo bayan fatawar da Moqtada al-Sadr ya baiwa magoya bayan sa na bijirewa gwamnati wajen halartar gangamin.

Duk da amincewa da shawarar masana kimiya wajen daukar matakan dakile yaduwar cutar, musamman fitattun mabiya addinin Yahudawa, wasu daga cikin limaman su sun bada shawara kan yadda za’a magance cutar.

Simcha Halevi Ashlag na daga cikin limaman da suka baiwa mabiyan su shawarar kwankwadar barasar da ake yi a Mexico da ake kira Corona domin cigaba da gudanar da ibadar su.

A sakon da ya aike na bidiyo, Ashlag yace idan sun yi addu’a suka kuma kwankwadi giyar, addu’ar su zata samu karfi sosai.

ma

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI