Coronavirus

Coronavirus ta kama sama da mutane dubu 300 bayan shiga kasashe 171

Wani bangaren New Delhi babban birnin kasar India bayan soma aikin takaita zirga-zirga saboda Coronavirus.
Wani bangaren New Delhi babban birnin kasar India bayan soma aikin takaita zirga-zirga saboda Coronavirus. AFP / Arun SANKAR

Adadin Mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a duniya ya karu zuwa 324,290, yayin da cutar ta shiga kasashen duniya 171, ta kuma kashe mutane 14, 396.

Talla

Alkaluman hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya sun ce adadin mutanen da suka kamu na iya zarce wadanda aka tabbatar, domin kuwa wasu kasashe suna kidaya wadanda aka kai asibiti ne kawai, sabanin duk wanda ya kamu da cutar.

Ya zuwa yanzu China tayi nasarar shawo kan cutar da ta barke a kasar ta, bayan ta kashe mutane 3,261 daga cikin mutane 81,054 da suka kamu da ita, yayin da 72,244 suka warke.

Kasar Italia yanzu ke matsayin na farko cikin kasashen da cutar tafi yin illa, bayan ta kashe mutane 5,476, yayin da ta kama mutane 59,138, kuma 7,024 sun warke.

A Spain mutane 1,720 suka mutu daga cikin 28,572 da suka kamu, sai Iran inda mutane 1,685 suka mutu daga cikin 21,638 da suka kamu, sai kuma Faransa mai dauke da mutane 16,018 da suka kamu, kuma 674 sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI