Coronavirus

Kasashe 50 sun killace fiye da mutane biliyan 1 saboda corona

Wani yanki na birnin Paris a Faransa da ke fuskantar killacewa saboda Coronavirus.
Wani yanki na birnin Paris a Faransa da ke fuskantar killacewa saboda Coronavirus. REUTERS/Christian Hartmann

Adadin mutanen da cutar Corona ta hallaka ya haura dubu 15 a kasashe 171 da ta fantsama dai dai lokacin da mahukunta suka tilastawa fiye da mutane biliyan guda zama a gida bayan haramta musu zirga-zirga, karkashin matakan da ake dauka na dakile yaduwar cutar.

Talla

Yanzu haka adadin wadanda cutar ta Corona ko kuma Covid-19 ta hallaka ya kai dubu 15 da 189 inda nahiyar Turai ke da adadin mamata dubu 9 da 197 mafiya yawansu ‘yan Italiya da adadin mutum dubu 5 da 476 kana Spain da mamata dubu 2 da 182.

Rahotanni sun bayyana cewa cikin sa’o’i 24 an samu karuwar mutane dubu 1 da 395 da cutar ta Corona ta hallaka cikin mutum dubu 172 da 238 da suka kamu da cutar, adadin da ke mayar da nahiyar Turai matsayin mafi yawan masu dauke da cutar haka zalika mafi saurin yaduwa.

Kawo yanzu fiye da mutane biliyan 1 aka tilastawa zama a gidaje ta hanyar haramta musu zirga-zirga duk dai a matakan dakile yaduwar cutar a kasashe 50 na duniya da cutar ta tsananta, ciki har da Faransa, Italy Argentina da Spain baya ga California a Amurka da Iran da Iraqi da kuma Rwanda, kana Birtaniya Colombia New Zealand da wani bangare na India.

Can a Spain tuni mahukunta suka kara adadin kwanakin ci gaba da kulle wasu sassa zuwa nan da ranar 11 ga watan Aprilu mai zuwa, bayanda aka samu huhawar wadanda suka kamu da cutar ciki har da jami’an lafiya dubu 3 da 910 galibi a birnin Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI