Saudiya ta kafa dokar hana zirga-zirga saboda Coronavirus
Sarkin Saudiya Salman bin AbdulAziz, ya sanar da kafa dokar hana zirga-zirga a fadin kasar, wadda yace ta soma aiki daga yau litinin, domin dakile yaduwar annobar murar Coronavirus.
Wallafawa ranar:
Karkashin dokar, an haramtawa daukacin al’ummar dake Saudiya fita daga karfe 7 na dare zuwa 6 na safe, har tsawon makwanni 3.
Gwamnatin Saudiya ta dauki matakin takaita zirga-zirgar ce bayanda adadin mutanen da suka kamu da cutar murar ya kai 511, koda yake kawo yanzu babu wanda ya mutu.
Dokar takaita zirga-zirgar dai bata shafi jami’an tsaro da na lafiya ba.
Tuni dai bullar annobar ta Coronavirus ta tilasa rufe gidajen Sinima, kasuwanni da gidajen abinci, sai kuma rufe filayen jiragen samanta bayan dakatar da zuwa Umrah.
Masarautar Saudiyan ta kuma dakatar yin Sallah a dukkanin Masallatan kasar, in banda mafiya daraja a duniya ba da suka hada da msallacin Harami dake birnin Makkah da kuma na Madina.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu