Cutar Coronavirus ta kama akalla mutane dubu 100 cikin kwanaki 4 - WHO

Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus. REUTERS/Denis Balibouse

Shugaban Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO Tedros Adhanom Gebreyesus, ya bayyana fargaba dangane da yadda cutar coronavirus ke yaduwa kamar wutar daji, inda ya bukaci cigaba da hadin kan kasashen duniya domin tinkarar matsalar.

Talla

A jawabin da ya yiwa manema labarai kan halin da ake ciki da kuma yadda ma’aikatan kula da lafiya ke sadaukar da rayukan su, Gebreyesus yace har ya zuwa yanzu babu maganin wannan cuta.

Shugaban na WHO yace bincike da alkalumman da suka tattara ya nuna cewar bayan barkewar annobar ta Coronavirus a China cikin watan Disamba, cutar ta kama mutane dubu 100 a sassan duniya cikin kwanaki 67, bayan kara karfi kuma sai annobar ta shafi karin wasu mutanen dubu 100 cikin kwanaki 11, yayinda kuma karin wasu dubu 100 suka kamu cikin kwanaki 4 kacal, abinda ya matukar tayarda hankalin duniya.

Yanzu haka dai wannan annoba ta halaka sama da mutane dubu 16, yayinda ta kama wasu sama da dubu 300 da 70, bayan kutsawa cikin kasashen akalla 170.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.