Bakonmu a Yau

Dakta Yusuf Abdu kan nazarin annobar Coronavirus

Sauti 03:33
Hoton fasalin yadda kwayar cutar Coronavirus take.
Hoton fasalin yadda kwayar cutar Coronavirus take. Getty Images

Masana Kiwon lafiya na cigaba da bayani ga jama’a da kuma janyo hankalin gwamnatoci kan matakan da ya dace a dauka wajen shawo kan annobar Coronavirus da ke cigaba da lakume rayuka.Ya zuwa yanzu cutar ta kashe mutane sama da 15,000 a kasashen duniya, yayinda ta fara dauki dai dai a Afirka.Wakilinmu Ibrahim Malam Goje ya tattauna da Dakta Yusuf Abdu, wani likita a Bauchi da yayi nazari akan cutar.