Kusan Mutum dubu 17 Coronavirus ta hallaka yau a sassan duniya
Wallafawa ranar:
Adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus zuwa tsakiyar ranar yau talata sun kai mutane dubu 16 da 961 a sassa daban daban na duniya.
A yanzu dai adadin wadanda ke dauke da wannan kwayar cuta ya kai dubu 386 da 353, yayin da tuni cutar ta shafi kasashen duniya 175.
A kasar Italiya ne aka fi samun wadanda suka rasa rayukansu, domin kuwa adadinsu ya kai dubu 6 da 77 a halin yanzu, yayin da China kasar da cutar ta samo asali ke biye ma ta da mamata dubu 3 da 270.
A can Spain sabbin alkaluma na tabbatar da cewa mutane dubu 2 da 696 ne suka mutu, yayin da a Iran cutar ta kashe mutane dubu daya da 934 zuwa tsakiyar ranar yau.
Ma’aikatar lafiya ta Faransa ta ce mutane 860 ne suka mutu daga cikin kusan dubu 20 da suka harbu da cutar, sai kuma Amurka mai yawan mamata 499.
Yanzu haka dai kusan mutane milyan dubu biyu ne ke kulle a gidansu a sassan duniya, sakamakon irin matakan da gwamnatoci ke dauka don hana yaduwar cutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu