Coronavirus-Duniya

Coronavirus ta shafi sama da kasashe 180

Wani jami'in kiwon lafiya na gudanar da gwaji don gano mutanen dake dauke da Coronavirus
Wani jami'in kiwon lafiya na gudanar da gwaji don gano mutanen dake dauke da Coronavirus AFP Photos/Michele Cattani

Alkalumman da hukumomin lafiya suka fitar a yau sun nuna adadin wadanda annobar murar coronavirus ta halaka da ya zarta dubu 19, gami da shafar wasu sama da dubu 400 da 20.Yanzu gaka dai wannan annoba ta shafi sama da kasashe 180.

Talla

Coronavirus ta ratsa kasashe 181, ta halaka mutane dubu 19 da 246, sama da dubu 400 da 27 da 940 kuma sun kamu da cutar murar alakakan.

Italiya ke kan gaba tsakanin kasashen da annobar ta coronavirus tafi kisa, inda bayan bullarta kasar ta lakume rayuka dubu 6 da 820, daga cikin dubu 69 da 176 da ta harba.

A kasa ta biyu da annobar tafi aika mutane lahira kuma itace Spain, inda rayukan mutane dubu 3 da 434 suka salwanta daga cikin jimillar dubu 47 da 610 da suka kamu da cutar.

Kasa ta uku da ta fi fuskantar kaifin annobar murar ita China, inda ta soma bulla. A Chinar annobar kashe mutane dubu 3 da 281 daga cikin dubu 81 da 218 da suka kamu.

Iran ke biye da China bayan rasa mutane dubu 2, da 77 ga annobar murar, daga cikin mutane dubu 27 da 17 da suka kamu, sai Faransa inda cutar ta kama mutane dubu 22 da 302, ta kuma halaka dubu 1 da 100.

A Amurka cutar coronavirus din ta kama mutane dubu 55 da 225, daga ciki kuma 600 sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.