Ko kun san adadin wadanda cutar coronavirus ta kashe a duniya ?

Jami'an 'yan sanda da na asibi dake yakar cutar coronavirus a kasar Spain
Jami'an 'yan sanda da na asibi dake yakar cutar coronavirus a kasar Spain PIERRE-PHILIPPE MARCOU / AFP

Adadin mutanen da cutar coronavirus ta kashe sun kai 18,259 a kasashen duniya 175, yayin da jami’an kiwon lafiya da gwamnatoci ke cigaba da tashi fadi wajen dakile yaduwar cutar.

Talla

Alkaluman masu dauke da cutar da aka tattara daga Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya sun ce mutane 404,020 suka kamu da cutar a kasashe 175 tun daga watan Disamba zuwa yanzu, yayin da 18,259 suka mutu.

Ya zuwa yanzu kasashen da akafi mutuwa a kowacce rana sune Italia wadda ta samu mutane 743 daga ranar Talata, sai Spain mai mamata 514 sannan Faransa mai mutane 240.

Ya zuwa yanzu mutane 6,820 suka mutu a Italia, 2,696 a Spain sai kuma 1,934 a Iran sai 1,100 a Faransa.

A nahiyar Turai, mutane 11,921 suka mutu, sai Asia mai mutane 3,573, sai Amurka da Canada mai mutane 624, Gabas ta Tsakiya na da mutane 1,972, kudancin Amurka da Caribbean na da mamata 98, sai Afirka mai 62, sannan Oceania mai mutane 9.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI