Amurka ta ware tukuicin dala miliyan 15 don kama Maduro

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro REUTERS/Fausto Torrealba

Ma'aikatar Shari'a Amurka ta sanar da tuhumar shugaban Venezuela Nicolas Maduro biza laifin ta’addanci da fataucin kwayoyi tare da tayin tukuicin dala miliyan 15 ga duk wanda ya bada bayanan da zasu kai ga kama shi.

Talla

Awani irin zargi mai tsaurin gaske da ba’a saba gani ko ji ba kan wani shugaban kasa, ma’aikatar shari’an na Amurka ta zargi shugaba Maduro na Venezuela da jagorantar wata kungiyar fataucin hodar Iblis da ake kira "Cartel of the Suns".

Masu binciken sun ce kungiyar da Maduro ke jagoranta ta yi aiki kafada da kafada da kungiyar 'yan tawayen Revolutionary Forces of Columbia wato (FARC), wacce Amurka ta sanya ta cikin kungiyoyin ta’addanci, tare da zarginta da fitar da daruruwan tan din din kwayoyi duk shekara.

Amurka na zargin Nicolas Maduro, wanda shine shugaban Venezuela tun a shekarar 2013, da wasu manyan jami'an gwamnatin sa da amfani da fudar iblis a matsayin makami na mamaye Amurka cikin shekaru 20 da suka gabata.

Ministan Shari’ar Amurka yace, "Sama da shekaru 20 kenan, Maduro da wasu manyan abokan sa da suke zargi da kulla yarjejeniya da FARC, lamarin da kai ga shigar da cocaine Amurka tare da lalata al’ummar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI