Coronavirus-Duniya

COVID-19 ta kama Boris Johnson da wasu fitattun mutane 5

Firaministan Birtaniya, Boris Johnson
Firaministan Birtaniya, Boris Johnson Julian Simmonds/Pool via REUTERS

Firaministan Birtaniya Boris Johnson tare da Sakataren kula da lafiyar kasar Matt Hancock sun zama fitattun mutanen baya bayan da suka kamu da cutar coronavirus ko kuma COVID-19 wadda yanzu haka ta kashe mutane sama da dubu 25 a duniya.

Talla

Firaminista Boris Johnson ya ce jiya Alhamis ya fara jin alamun cutar a jikin sa abinda ya sa aka masa gwaji aka kuma tabbatar da cewar ya kamu da ita kamar yadda ya bayyana a sakon bidiyo.

Johnson ya ce yanzu haka ya killace kan sa kuma zai cigaba da jagorancin gwamnati wajen shawo kan cutar wadda ta kama mutane 14,579 ta kuma kashe 759 a Birtaniya.

Daga cikin fitattun mutanen da suka kamu da wannan cuta sun hada da Yarima Charles mai jiran gadon Sarautar Birtaniya da Sarki Albert na II da ke Monaco da Michel Barnier, jagoran tattaunawar kungiyar kasashen Turai, yayinda Firaministan Canada Justin Trudeau ya killace kan sa saboda kamuwar matarsa, kamar yadda Angela Merkel shugabar gwamnatin Jamus ta yi bayan gwajin da aka mata ya ce bata dauke da cutar.

Ita dai wannan cuta da bata bar talakawa ba ballantana shugabanni ta hallaka fitaccen mawakin Afirka Manu Dibango, yayinda ta kama ministoci da gwamnoni da jami’an gwamnati a sassa daban daban na duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.