Coronavirus-Duniya

Kusan mutum dubu 26 Coronavirus ta hallaka yau a sassan duniya

Wajen adana gawarwakin da coronavirus ta hallaka a nahiyar Turai.
Wajen adana gawarwakin da coronavirus ta hallaka a nahiyar Turai. AFP/Belga/Benoit Doppagne

Kusan mutum dubu 26 cutar COVID-19 ta hallaka yau juma’a a sassa daban-daban na duniya yayinda ake da jumullar mutane fiye da dubu dari 5 da cutar ta kama a kasashe 183 galibinsu a nahiyar turai wadda yanzu haka ta dara China a yawan mutanen da cutar ta hallaka.

Talla

Kafin karfe 12 na ranar yau juma’a yankin turai ne ke ci gaba da kasancewa sahun gaba ta fannin wadanda suka fi rasa rayukansu sakamakon cutar da mutane kusan dubu 18, sai Asiya mai mutane dudu 3 da 682 yayin da Yankin Gabas ta Tsakiya ke da yawan mamata dubu 2 437.

Kasashen Amurka da Canada kuwa na da yawan mamata dubu 1 da 332, Latin Amurka da Karibiyan 182 sai kuma Afirka mai mutane 91.

Kasar Italy ita ce kan gaba wajen yawan mutanen da cutar ta hallaka a yau da mutum dari 9 da 69 kana Spain da jumullar mutum 769 cikin mutane dubu 64 da 59 da ke dauke da cutar, adadin da ya mayar da yawan wadanda cutar ta kashe tun bayan barkewarta a kasar zuwa yau, mutum dubu 4 da 800.

Yanzu haka Spain din ita ke matsayin ta biyu a yawan wadanda cutar ta coronavirus ta hallaka kasa da Italy wadda ke da jumullar mutane dubu 8 da 165 bayan a jiya ta kashe mutane 662, yayinda a yanzu haka ake da mutum dubu 8 sabbin kamuwa.

Iran wadda ke matsayin ta 4 a yawan wadanda cutar ta hallaka na da jumullar mutane dubu 2 da 378 kasa da China wadda ke matsayin ta 3 a jerin yawan mamata da jumullar mutane dubu 3 da 292 baya sabbin kamuwa mutum 55 kana Faransa a matsayin ta biyar da jumullar mamata dubu 1 da 696.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI