Coronavirus ta halaka mutane sama da dubu 27 a kasashe 183
Alkalumman hukumomin lafiya sun ce daga jiya asabar zuwa yau lahadi, adadin wadanda annobar murar coronavirus ta halaka ya karu daga dubu 25 zuwa dubu 27 da 989 a fadin duniya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yanzu haka adadin wadanda suka kamu da cutar murar da ta soma bulla a China, ya haura dubu 605, da 220 bayan da annobar da shiga kasashe 183.
Zuwa yanzu kuma hukumomin lafiyar sun tabbatar da cewar daga cikin sama da dubu 605 din da suka kamu da cutar, dubu 129 da 100 sun warke sarai.
A Italiya inda annobar ta soma halaka rai cikin Fabarairu, a yanzu haka annobar ta coronavirus ta lakume rayuka dubu 9 da 134, yayinda wasu dubu 86 da 498 suka kamu, daga ciki kuma dubu 10 da 950 sun samu waraka.
Kasar Spain da a yanzu ta zarta China wajen asarar rayuka dalilin wannan annoba, mutane 800 da 32 ta rasa cikin kwana 1, abinda ya sanya zuwa yau annobar ta halaka jimillar mutane dubu 5 da 690, sai kuma dubu 72 da 238 da suka kamu da cutar.
A China kuwa inda annobar murar ta soma bulla, mutane dubu 3 da 295 suka mutu, yayinda dubu 81 da 394 suka kamu da cutar, daga ciki kuma dubu 74 da 971 sun warke.
Sauran kasashen da annobar ta coronavirus ta yi muni cikinsu, sun hada da Iran, inda cutar ta halaka mutane dubu 2 da 517 wasu dubu 35 da 408 kuma suka kamu, mutane 139 suka halaka cikin kwana 1 a kasar ta Iran, yayinda a Faransa mutane dubu 1 da 995 suka mutu, wasu dubu 32 da 964 kuma suka kamu.
Amurka da a yanzu ta zarta kowace kasa adadin wadanda annobar ta shafa, mutane dubu 1 da 711 suka mutu, yayinda dubu 104 da 837 suka kamu da cutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu