Duniya

Coronavirus ta halaka sama da mutane dubu 30 a kasa da watanni 4

Yankin Las Ramblas a birnin Barcelona dake Spain, bayan soma aikin dokar hana fita. 16/3/2020.
Yankin Las Ramblas a birnin Barcelona dake Spain, bayan soma aikin dokar hana fita. 16/3/2020. REUTERS/Nacho Doce

Hukumomin lafiya sun ce a halin yanzu annobar coronavirus ta halaka sama da mutane dubu 30 a fadin duniya, tun bayan bullarta a kasar China cikin watan disamban shekarar bara.

Talla

Kididdigar ta nuna cewar kashi 2 bisa 3 na adadin rayukan dubu 30 da 3, sun salwanta ne a nahiyar Turai, kuma Italiya kadai ke da kashi 1 bisa 3, bayan mutuwar sama da mutane dubu 10 dalilin cutar a kasar.

A bangaren wadanda annobar ta shafa kuwa, a yanzu adadinsu ya haura dubu 640 da 770 a fadin duniya, bayan shiga kasashe da manyan yankuna 183.

Zuwa yanzu dai kasashen da annobar at fi muni a cikinsu sun hada da Italiya, inda kamar yadda aka ji mutane dubu 10 da 23 suka mutu, sai Spain, inda cutar ta kashe mutane dubu 5 da 690, bayan halaka mutane 838 a rana guda, sai kuma China da ta rasa mutane dubu 3 da 295.

A Iran inda a jiya kadai mutane 123 suka mutu, a yanzu jimillar wadanda annobar ta halaka a kasar ya kai dubu 2 da 517, sai kuam Faransa inda cutar ta lakume rayuka dubu 2 da 314.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.