Coronavirus

Coronavirus ta yi abin da ta saba yi a kasashen duniya

Jami'an yaki da cutar Coronavirus
Jami'an yaki da cutar Coronavirus AFP

Sama da mutane dubu 720 sun kamu da cutar Coronavirus ko kuma Covid-19 wadda kawo yanzu ta lakume rayuka kusan dubu 35 a kasashen duniya 183 tun bayan barkewarta a karshen shekarar bara a China.

Talla

Kasar Italiya na da mutane dubu 10 da 779 da cutar Coronavirus ta aika lahira, yayin da mutane dubu 97 da 689 suka kamu da ita a kasar.

Spain ta yi asarar mutane dubu 7 da 340 daga cikin mutane dubu 85 da 195 da Coronavirus ta harba, yayin da China wadda ta kasance makyankyasar wannan annuba, ta rasa mutane dubu 3 da 304 kacal.

Iran ta rasa mutane dubu 2 da 757 daga cikin mutane dubu 41 da 495 da cutar ta kama. Sai kuma Faransa da ta yi bankawana da mutane dubu 2 da 606 a sanadiyar cutar.

A can Girka kuwa, wata dattijuwa da ta haura shekaru 70 ta zama ta farko da cutar ta Covid 19 ta kashe a kasar.

A wannan Litinin ne Moscow ta fara aiwatar da dokar hana zirga-zirgar jama’a har sai baba ta gani bayan an samu jumullar mutane dubu 1 da 534 da suka kamu da wannan cuta a Rasha, inda takwas daga cikinsu suka sheka lahira.

Wannan annuba dai ta sa an tilasta wa sama da mutane biliyan 3.4 a kusan kasashen duniya 80 zaman gida, wato kwatankwacin kashi 43 cikin 100 na al’ummar duniya baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI