Coronavirus-Duniya

Covid-19-Adadin mamata ya zarta dubu 33 a sassan duniya

Jami'an kiwon lafiya a fagen yaki da Coronavirus
Jami'an kiwon lafiya a fagen yaki da Coronavirus RFI/Stéphane Lagarde

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar coronavirus ko kuma COVID-19 ya zarce 33,000 zuwa safiyar wannan litinin, yayin da kasashen duniya ke ta fafutukar shawo kan annobar.

Talla

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da suka kamu da wannan cuta ta COVID-19 a duniya ya zarce 697,750 a kasashen duniya 183 da kuma wasu yankuna, tun bayan barkewar cutar a China a watan Disambar bara, kuma daga cikin wannan adadi, 137,900 sun warke.

Kasar Italiya ke sahun gaba cikin kasashen da suka fi fuskantar wannan annoba, sakamakon mutuwar mutane 10,779 daga cikin 97,689 da suka kamu da ita, kana 13,030 sun warke, sai kuma Spain wanda a jiya kawai mutane 838 suka mutu cikin sa’o’i 24, abin da ya kawo adadin wadanda suka mutu a kasar zuwa 6,803.

A faransa mutane 2,606 suka mutu daga cikin 38,309 da suka kamu, sai Iran wadda ta yi asarar mutane 2,640 daga cikin 38,309 da suka kamu.

A Amurka mutane 2,351 suka mutu daga cikin 132,637 da suka kamu, yayin da 2,612 suka warke.

A Afirka kuwa mutane 142 suka mutu daga cikin 4,569 da suka kamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.