Coronavirus

Coronavirus ba ta kyale matasa ba

Wasu matasa sanye da kyallen rufe hanci don kauce wa kamuwa da Coronavirus
Wasu matasa sanye da kyallen rufe hanci don kauce wa kamuwa da Coronavirus AFP/Ted ALJIBE

Wani binciken masana a Birtaniya ya nuna cewar sabanin yadda aka zata a baya cewar masu yawan shekaru ne kawai cutar COVID-19 tafi yi wa illa, yanzu haka mutanen da ke matsakaitan shekaru na fuskantar illar cutar wadda ke iya hallaka su.

Talla

Masanan na Birtaniya sun gudanar da binciken ne akan mutane 3,600 da aka tabbatar sun kamu da cutar da kuma bayanan wasu daruruwan fasinjojin da suka fito daga Wuhan da ke kasar China, inda suka gano cewar shekaru na matukar tasiri wajen fuskantar illar cutar, inda kusan kowanne mutun guda daga cikin mutane 5 da ke da shekaru sama da 80 ke bukatar kwantar da shi a asibiti.

Azra Ghani na Cibiyar Binciken Imperial da ke London kuma daya daga cikin wadanda suka jagoranci binciken ya ce, bincikensu na iya tasiri a kowacce kasa.

Ghani ya ce, binciken nasu ya nuna cewar masu shekaru 50 zuwa sama sun fi bukatar kwantar da su a asibiti idan sun kamu da cutar, sabanin masu shekaru kasa da 50.

Yanzu haka hukumomi a kasashen duniya sun tilasta wa biliyoyin mutane zama a cikin gidajensu domin dakile yaduwar wannan annoba ta COVID-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.