Coronavirus

Coronavirus ta aika mutane dubu 36 lahira

Akwatin gawarwakin mutanen da suka mutu a sanadiyar Coronavirus a Italiya
Akwatin gawarwakin mutanen da suka mutu a sanadiyar Coronavirus a Italiya Reuters

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon annubar COVID-19 ya zarce 36,000 yayin da kasashen duniya ke ci gaba da fafutukar tinkarar matsalar.

Talla

Sama da kashi biyu bisa uku na mutanen da suka mutu sakamakon wannan cuta sun fito ne daga nahiyar Turai, abin da ya sa shugaba Donald Trump ya ce, zai aika da kayan kula da lafiya zuwa kasashen Italiya da Faransa da kuma Spain.

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, yawan mutanen da suka kamu da wannan annuba da ta mamaye kasashen duniya ya kai 757,940 a kasashe 184 tun bayan barkewarta a watan Disamban bara, yayin da akalla 148,700 suka warke, kana 36,674 suka mutu.

Italiya ke matsayi na farko na yawan mutanen da suka mutu, inda take da mutane 11,591 daga cikin 101,739 da suka kamu, yayin da 14,620 suka warke.

Kasar Spain ke matsayi na biyu da mutane 7,340 da suka mutu, cikinsu har da 812 da suka mutu a jiya kawai, daga cikin 85,195 da suka kamu. sai Faransa wadda ta yi asarar mutane 3,024 daga cikin 44,550 da suka kamu.

Kasar Amurka yanzu ke matsayi na farko na mutanen da suka kamu, inda suka kai 153,246, yayin da 2,828 suka mutu, kana 5,545 suka warke.

Daga cikin mutane 36,674 da suka mutu a duniya, 26,543 sun fito ne daga nahiyar Turai, sai Asiya mai mutane 3,837, sai Gabas ta Tsakiya mai 2,856 sai Afrika mai 163.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI