Coronavirus

Coronavirus ta doshi lakume rayuka dubu 40

Adadin wadanda cutar Covid-19 ta kashe ya kai mutane 38,466 kafin tsakiyar ranar yau talata, yayin da kasashen duniya ke ci gaba da daukar matakai daban daban don yaki da wannan annoba.

Akwatin gawarwakin mutanen da suka mutu a sanadiyar Coronavirus a Italiya
Akwatin gawarwakin mutanen da suka mutu a sanadiyar Coronavirus a Italiya Reuters
Talla

Sama da mutane dubu 791 ne suka harbu da kwayar cutar a kasashe 185 na duniya daga lokacin da ta bulla cikin watan disambar da ya gabata a China, to sai dai sabbin alkaluman na nuni da cewa sama da mutane dubu 163 sun warke daga cutar.

A Italiya an samu asarar rayukan mutane 11,591 daga cikin mutane 101,739 da suka harbu da ita, yayin da aka sallami wasu 14,620 bayan sun warke.

Spain ce kasa ta biyu inda Covid-19 ta fi yi wa illa da asarar rayukan mutane8,189 inda a cikin sa’o’i 24 na baya-bayan nan aka samu asarar rayuka 849.

A can kuwa China adadin mamatan ya tashi zuwa 3,0305 amma ba tare da an hada wadanda suka rasu a Hong Kong da tsibirin Macau ba.

A Faransa an samu asarar rayuka 3,024, sai Amurka ida mutane 3,170 suka rasa rayukansu. A nahiyar Afirka adadin mamatan ya tashi zuwa 170 zuwa tsakiyar ranar yau talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI