Faransa

Coronavirus ta kashe Faransawa 418 cikin kwana daya

Jami'an yaki da cutar Coronavirus a Faransa
Jami'an yaki da cutar Coronavirus a Faransa JEAN-CHRISTOPHE VERHAEGEN / AFP

Hukumomin lafiyar Faransa sun ce, an samu sabbin mutane 418 da cutar Coronavirus ta kashe a cikin sa’o’i 24, yayin da a jumulce cutar ta kashe mutane dubu 3 da 24 a kasar.

Talla

Kodayake an tattara alkaluman ne a asibitoci, inda mahukuntan kasar ke cewa, akwai wadadna cutar ta kashe a gidajensu amma ba a yi rajistan su ba.

Faransa ce kasa ta hudu da wannan annuba ta fi kisa bayan Italiya da Spain da kuma China.

Kusan mutane dubu 21 ne ke kwance a asibiti, inda daga ranar Lahadi zuwa jiya Litanin aka samu Karin mutane dubu 1, 592.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.