Faransa

Macron ya ware wa Coronavirus Euro biliyan 4

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Pascal Rossignol

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya sanar da ware Euro bilyan 4 don samar da kayayyakin kariya daga cutar Covid-19 a cikin gaggawa, da suka hada da na’urarar taimakawa marasa lafiya yin numfashi, da sabulun wanke hannuwa da kuma kyallayen rufe baki da hanci, wadanda suka yi karanci a kasar.

Talla

Macron ya ce, suna bukatar akalla kyallayen rufe baki da hanci milyan 40 a kowanne mako kuma tuni suka yi odar  kyallaye har guda milyan dubu daya daga China da wasu kasashe.

Sai dai kafin isowar wadannan kayayyaki, ko shakka babu su ma kansu jami’an kiwon lafiya na cikin yanayi na bukata a cewar Macon.

"Kafin barkewar wannan cuta, ana sarrafa kyallayen rufe baki da hanci milyan uku da dubu 300 ne a mako, amma ya zama wajibi kafin karshen watan Afrilu mu iya sarrafa guda milyan 15 a mako". Inji Macron.

Shugaban ya kara da cerwa "wani babban kalubale da ke gabanmu shi ne samar da na’urar taimaka wa numfashi, yanzu haka mun yi odar irin wadannan na’urori daga kasashen Turai da kuma kamfani daya da ke kera su a cikin gida Faransa mai suna Air Liquide, kamfanin da muke fatan zai iya sarrafa na’urar numfashi dubu 10 kafin tsakiyar watan Mayu."

Sai kuma ruwan sabulun kashe kwayoyin cuta don wanke hannuwa, a maimakon sarrafa lita dubu 40 muna fatan rubanya adadin zuwa lita dubu 500 a rana a cewar shugaban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.