Saudiya

Saudiya ta bukaci Musulmai su jinkirta aikin hajjin bana

Mahajjata da ke dawafi a masallacin Ka'aba na Saudiya
Mahajjata da ke dawafi a masallacin Ka'aba na Saudiya FETHI BELAID / AFP

Kasar Saudi Arabia ta bukaci Musulmin duniya da su jinkirta shirin zuwa hajjin bana saboda rashin tabbas dangane da annubar Coronavirus.

Talla

Ministan Kula da Ayyukan Hajji, Mohammed Benten ya sanar da haka, inda yake cewa Saudiya a shirye take ta karbi masu zuwa hajji da Umrah a kodayaushe, amma halin da ake ciki na annubar coronavirus, ya zama dole ta kare lafiyar Musulmin duniya.

Ya zuwa yanzu, Saudiyar ba ta bayyana ko za a iya gudanar da ibadar hajjin banan ba da ake saran yi a watan Yuli mai zuwa.

Akalla Musulmin duniya sama da miliyan biyu da rabi ke zuwa hajji kowacce shekara domin sauke farali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI