Iran-EU

Turai ta taimaka wa Iran duk da takunkumin Amurka

Wasu masu jinyar Coronavirus a Iran
Wasu masu jinyar Coronavirus a Iran aparat.com/ mahlatm

Tarayyar Turai ta aika wa Iran kayayyakin kiwon lafiya a karkashin yarjejeniyar 'Instex' da ta bada damar kewaye takunkuman da Amurka ta lafta wa kasar.

Talla

Kasashen Faransa da Jamus da Britaniya sun bayyana cewa, shirin na Intex ya yi nasara a zangon farko wajen isar da kayayyakin jinya daga Turai zuwa Iran kamar yadda  Ma'aikatar Harakokin Wajen Jamus ta tabbatar.

Sanarwa ta ci gaba da cewa, shirin na Intex zai ci gaba da isar da wasu kayayyaki ga Iran.

Kakakin Ma'aikatar Harakokin Wajen Iran ya ce, a ranar 14 ga wannan wata na Maris, kasar ta karbi taimakon kayayyakin jinya da magunguna daga hannun kasashen Jamus da Azerbejan da China da Daular Larabwa da Faransa da Birtaniya da Japan Qatar da Rasha da kuma Turkiya.

Iran ta ce, ba za ta taba mantawa da aminanta a lokutan kunci ba, kamar irin  wannan lokacin da cutar Coronavirus ta hallaka Iraniyawa  2,757.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI