Coronavirus

Coronavirus ta kashe tsohon shugaban Marseille

Marigayi  Pape Diouf ya zama mutun na farko da coronavirus ta kashe a Senegal
Marigayi Pape Diouf ya zama mutun na farko da coronavirus ta kashe a Senegal Anne-Christine POUJOULAT / AFP

Tsohon shugaban Kungiyar Kwallon Kafar Olympic Marseille da ke Faransa kuma dan assalin kasar Senegal, Papa Diouf ya rasu bayan kamuwa da cutar coronavirus.

Talla

Diouf ya mutu yana da shekaru 68 bayan kamuwa da cutar coroanavirus kamar yadda danginsa suka sanar.

Marigayin wanda aka haifa a kasar Chadi, na da takardar shaidar zama dan kasa a Faransa da kuma Senegal.

An kwantar da shi ne a asibitin birnin Dakar  bayan ya kamu da coronavirus, yayin da ya zama mutun na farko da cutar ta aika lahira a Senegal.

Diouf ya jagoranci kungiyar Marseille tsakanin shekarar 2005 zuwa 2009, sannan ya taimaka wajen gina kungiyar har ta lashe kofin gasar Lig 1 a 2010.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI