Coronavirus

Ko kun san rabin mutanen duniya na killace a gidajensu?

Wani bangare na birnin New York na Amurka da ya kasance wayam saboda coronavirus
Wani bangare na birnin New York na Amurka da ya kasance wayam saboda coronavirus Reuters

Wani bincike ya nuna cewa yanzu haka cutar COVID-19 ta tilasta killace rabin mutanen duniya da adadinsu ya kai biliyan 4 a gidajensu, domin dakile yaduwar cutar a kasashe sama da 180.

Talla

Binciken ya ce, matakin ya hada da wadanda aka tilasata wa zaman gida na dole da wadanda aka bai wa shawarar zama a gida da kuma wadanda aka killace a kasashe 90.

A Philippines, shugaban kasar Rodrigo Duterte har umurnin harbi ya bayar muddin jami’an tsaro suka ga wanda ya karya dokar hana fitar, yayin da cutar coronavirus ta kashe mutane sama da 50,000 a duniya.

Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa, a halin yanzu, matakin tilasta wa mutane zaman gida, shi ne mafi a'ala wajen yaki da cutar coronavirus, lura da cewa, har yanzu ba a gano takamamman maganinta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.