Saudiya

Saudiya ta hana zirga-zirga a Makka da Madina

Matakin hana zirga-zirgar ya dada haifar da shakku kan yiwuwar gudanar da aikin hajjin bana
Matakin hana zirga-zirgar ya dada haifar da shakku kan yiwuwar gudanar da aikin hajjin bana Reuters

Saudi Arabia ta tsawaita dokar hana zirga-zirga zuwa sa’oi 24 a biranen Makkah da Madinah domin dakile yaduwar cutar coronavirus wadda ta kashe mutane 21 a kasar.

Talla

Ma’aikatar Cikin Gidan kasar ta ce, daga ranar Alhamis (wato jiya)  mazauna biranen biyu za su zauna a gidajensu na tsawon sa’o'i 24 sabanin sa’o'i 15 da aka sanar a baya.

Wannan dokar hana fita a manyan biranen biyu masu tsarki za su ci gaba da aiki har sai baba-ta-gani.

Wannan sanarwar ta dada jefa shakku dangane da shirin aikin hajjin bana, wanda gwamnatin kasar ta umurci kasashen Musulmi na duniya da su dakatar da shirye-shiryensu saboda yanayin da ake ciki na wannan annoba ta coronavirus.

Kimanin Musulmin duniya miliyan 2 da rabi ke zuwa Makkah da Madina domin sauke farali a kowacce shekara.

Tuni Saudiyar ta dakatar da aikin umara da zummar dakile wannan cuta mai ci gaba da yaduwa cikin sauri.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.