Coronavirus-Duniya

Kusan mutane dubu 58 Covid-19 ta kashe a duniya

Jami'an kiwon lafiya na kokarin ceto rayukan wadanda suka kamu da Covid-19
Jami'an kiwon lafiya na kokarin ceto rayukan wadanda suka kamu da Covid-19 Reuters

Kasashe na ci gaba da daukar matakai don yaki da annobar Coronavirus, wadda alkaluma na baya-bayan nan ke nuni da cewa adadin wadanda suka kamu da ita sun haura milyan daya da dubu 82 a sassan duniya.

Talla

Tuni dai cutar ta kashe mutane dubu 57 da 474 a cikin kasashe 188, kuma Italiya ce ke matsayin kasar da wannan annoba ta fi yi wa ta’adi da yawan mamata dubu 14 da 681, yayin da Spain ke matsayin ta biyu da yawan mamata dubu 10 da 935, sai kuma Amurka inda mutane dubu 6 da 700 suka rasa rayukansu, yayin da a Faransa adadin mamatan ya tashi zuwa dubu 6 da 507.

A yau asabar, an gudanar da adu’o’I na musamman don tunawa da mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon Corona a China, kasar da cutar ta samo asali tare da kashe mutane dubu 3 da 300 kafin rage karfin yaduwarta.

A birnin Wuhan mai mutane milyan 11 inda cutar ta fara, mutane sun tsaya cik kan tituna da misalin karfe 10 na safiyar lokacin da aka tayar da jiniya don tunawa da wadanda suka rasa rayukansu, yayin da aka gudanar da wasu adu’o’i na musamman a asibitin Tongji, inda aka yi jinya mutum na farko da ya kamu da cutar.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.