Pakistan

An killace Musulmai dubu 20 saboda coronavirus

Pakistan ta killace Musulmai dubu 20, sannan kuma tana ci gaba da neman karin dubbai da suka halarci wani taron addinin Islama a birnin Lahore a daidai lokacin da annobar coronavirus ta kazance a duniya.

Sama da mutane dubu 100 ne suka halarci taron na Pakistan
Sama da mutane dubu 100 ne suka halarci taron na Pakistan bangkokpost
Talla

Tuni gwajin da aka yi wa wasu daga cikin mahalarta taron ya nuna cewa , 154 sun kamu da cutar coronavirus, inda kuma biyu suka riga mu gidan gaskiya, kamar yadda hukumomin kasar suka shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP.

Rahotanni sun ce, sama da mabiya akidar dubu 100 ne suka halarci taron daga sassan duniya da suka hada da Najeriya da China da Idonesia da Afghanistan, yayin da akasarinsu suka koma kasashensu na asali ba tare da tantance su ba.

Mabiya akidar ta Tablighi sun gudanar da taron ne tsakanin ranakun 10-12 na watan Maris da ya gabata.

Kazalika hukumomin kasar ta Pakistan sun kulle Masallatan mabiya akidar ta Tablighi a kasar.

Kawo yanzu coronavirus ta kashe mutane a kalla 45 a Pakistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI