Coronavirus-Duniya

Mutane sama da dubu 65 sun mutu bayan kamuwa da coronavirus

Wasu daga cikin kaburburan mutanen da coronavirus ta kashe a Amurka
Wasu daga cikin kaburburan mutanen da coronavirus ta kashe a Amurka Reuters

Annobar Covid-19 ta kasahe sama da mutane dubu 65 a sassan duniya, yayin da kasashe ke ci da daukar matakai daban daban don yaki da wannan annoba.

Talla

Yanzu haka mutane dubu 65 da 272 a sassan duniya ne suka mutu a sanadiyar cutar kuma har yanzu Italiya ce ke matsayin kasa ta farko da cutar ta fi yin kisa saboda an rasa mutane dubu 15 da 362 zuwa tsakiyar ranar yau Lahadi.

Spain ce kasa ta biyu da wannan annoba ta kashe mutane masu tarin yawa, domin kuwa alkaluma Ma’aikatar Lafiyar Kasar na nuni da cewa mutane dubu 12 da 418 ne suka rasa rayukansu kawo yanzu.

Amurka ke matsayin ta uku da mutane dubu 8 da 503, sannan Faransa mai mamata dubu 7 da 560, yayin da Birtaniya ke biye masu da mutane dubu da 313 da suka rasu.

A yankin Turai ne wannan annoba ta Coronavirus, ta fi yin kisa, inda alkaluma na baya-bayan nan suka tabbatar da cewa cutar ta kashe sama da mutane dubu 45 a yankin kawai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.