Coronavirus

'Hassada ce ta sa ake alakanta 5G da cutar coronavirus'

China ta kaddamar da fasahar 5G tare da hadin guiwar Kamfanin Sadarwar Huawei
China ta kaddamar da fasahar 5G tare da hadin guiwar Kamfanin Sadarwar Huawei Reuters

Ana ci gaba da tafka muhawara a kasashen duniya game da alaka tsakanin annobar coronavirus da hanyar sadarwar 5G, inda wasu ke da yakinin cewa, tabbas wannan sabuwar fasahar ta 5G, ita ce silar barkewar coronavirus wadda ta lakume rayuka kusan dubu 70 a sassan duniya. Sai dai wasu masana harkar sadarwar sun ce, ko kadan babu abin da ya danganta cutar da 5G.

Talla

A zantawarsa da sashen hausa na RFI, Umar Saleh Gwani, masanin fasahar sadarwa a Najeriya, ya ce, babu alaka tsakanin wannan annoba da hanyar sadarwar 5G, hasali ma, hassadar da ake yi wa China ce, ta sa wasu ke alakanta cutar da 5G.

Kuna latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da Ibrahim Malam-Goje ya yi da Umar Saleh Gwani kan wannan takaddama.

'Hassada ce ta sa ake alakanta 5G da cutar coronavirus'

Gwani ya bayyana cewa, a baya-bayan nan, kasar China ta yi wa takwarorinta irin su Amurka da kasashen Turai fintinkau a bangarorin kimiya da fasaha da kere-keren makamai na zamani har ma da harkar kasuwanci, abin da ya sa ake yi wa Chinan zagon kasa bayan ta kaddamar da gagarumar fasahar 5G tare da hadin guiwar kamfanin Huawei.

A cewar masanin, fintinkau din da China ta yi wa manyan kasashen duniya, ya girgiza ginshikin tsarin jari hujja a duniya, lamarin da ya yi sanadiyar karyewar hada-hadar kasuwanci a hannayen jari na Wall Street dake birnin New York na Amurka a cewarsa.

Da dama daga cikin mutane sun yi amanna cewa, 5G ne silar barkewar coronavirus, inda har a Birtaniya, wasu matasa suka fusata har suka yi ta tumbuke turakun sadarwar  a kasar.

Ana sa ran nan gaba masana za su fito su kara yi wa duniya bayani kan alakr 5G da cutar coronavirus ko kuma covid-19.

'Hassada ce ta sa ake alakanta 5G da cutar coronavirus'

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.