Coronavirus-Ingila

Za mu ci galaba kan coronavirus- Sarauniyar Ingila

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II a yayin jawabi ga al'ummar Birtaniya
Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II a yayin jawabi ga al'ummar Birtaniya Reuters

A wani jawabin nuna goyon baya da aka watsa ta kafar talabijin, Sarauniyar Ingila, Elizabeth ta II ta bayyana cewa, kasar za ta yi nasara a yakin da take yi da annobar coronavirus, yayin da ta jinjina wa ma'aikatan kiwon lafiyar kasar da suka sadaukar da rayuwansu wajen ceto masu dauke da wannan cuta.

Talla

A jawabinta da ba a saba ganin irinsa ba, Sarauniyar mai shekaru 93 ta mika godiya ga al’ummar Birtaniya bisa biyayyarsu ga dokar hana fita da gwamnati ta kafa don dakile yaduwar cutar.

Jawabin nata na zuwa ne a daidai lokacin da coronavirus ta kashe mutane kimanin dubu 5 a Ingila.

"Ina yaba wa kowa da kowa daga cikin jami’an kiwon lafiya na NHS, tare da masu kula da jama’a da masu gudanar da ayyuka na musamman, wadanda ke gudanar da aikinsu na yau da kullum da sadaukar da kai a wajen gidajensu, domin taimaka mana baki daya." Inji Sarauniya.

Elizabeth ta kara da cewa, "muna shawo kan wannan cuta tare, kuma ina jaddada muku cewar, idan muka hada kai muka kuma jajirce zamu samu nasara."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.