Coronavirus

WHO ta fusata kan wariyar launin da aka nuna wa Afrika

Afrika ba fagen gwaje-gwajen maganin riga-kafin coronavirus ba ne.
Afrika ba fagen gwaje-gwajen maganin riga-kafin coronavirus ba ne. NIAID

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO cikin fushi, ta caccaki kalaman da wasu masana kimiya suka furta, inda suka bada shawarar gwajin maganin riga-kafin cutar coronavirus kan al’ummar Afrika.

Talla

Shugaban Hukumar Lafiyar ta WHO, Tedros Adhanom Ghenreyesus ya bayyana wadannan kalamai a matsayin wariyar launin fata, yana mai cewa, nahiyar Afrika ba za ta kasance fagen gwaje-gwajen duk wani maganin riga-kafi ba.

Ghebreyesu ya ce, za su bi dukkanin dokokin kimiya da suka bada damar gwajin riga-kafi a kowacce nahiya ta duniya.

Wasu likitocin Faransa biyu ne suka bada shawarar fara gwajin maganin riga-kafin coronavirus kan al'ummar Afrika don sanin tasirinsa, abin da ya janyo musu caccaka daga sassan duniya.

Daga cikin wadanda suka mayar wa da likitocin martani har da tsohon fitaccen dan wasan kwallon kafar Ivory Coast, Didier Drogba wanda ya ce, Afrika ba dakin gwaje-gwajen kimiya ba ne, inda ya bayyana kalamansu a matsayin wariyar launin fata.

Shi ma Olivier Faure na jam'iyyar Socialist ta Faransa, ya ce, mutanen Afrika ba beraye ba ne da Turawa za su rika amfani da su wajen gwaje-gwajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.