Coronavirus

WhatsApp ta dauki mataki kan coronavirus

Ana amfani da WhatsApp  wajen yada labaran karya masu haddasa fitina a tsakanin al'umma
Ana amfani da WhatsApp wajen yada labaran karya masu haddasa fitina a tsakanin al'umma Reuters

Kamfanin WhatsApp ya takaita sakwannin da masu amfani da manhajar za su iya turawa, a wani mataki na rage yada labaran karya game da annobar coronavirus da ta zame wa duniya alakakai. 

Talla

Makasudin wannan manufa ta WhatsApp shi ne, kayyade yawan sakonnin da ake iya turawa a lokaci guda, inda a yanzu kamfanin ya bada damar tura sako guda ga mutun guda a lokaci guda.

An dauki matakin ne da zummar rage labarai masu tayar da hankali kuma watakila na kanzon kurege.

A makwannin da suka wuce, an samu karuwar sakwannin da ake yadawa a dandalin WhatsApp, abin da ya sa wasu daga cikin masu amfani da manhajar suka koka.

A shakarar da ta gabata, kamfanin WhatsApp ya kayyade yawan sakwannin da ake iya yadawa zuwa 5 a lokaci guda don dakile yaduwar labarai barkatai, biyo bayan tashin hankalin da aka samu a kasar India bayan yada wasu labarai da suka haddasa tashin hankali a kasar.

WhatsApp, wanda ke da sama da mutane biliyan daya da ke amfani da manhajarsa a fadin duniya, ya zama kafa mai mahimmanci na samun labarai a wannan lokaci da duniya ke fama da  annobar COVID 19, yayin da wasu mutane ke yada labaran karya game da annobar.

Daya daga cikin labaran karyar da aka yi ta yadawa a wannan kafa, sun hada da labaran da ke alakanta cutar coronavirus da sabuwar fasahar sadarwa ta 5G, labarin da mutane da dama suka yi amanna da shi, alhali kuwa karya ne kamar yadda masana kimiya suka yi fashin baki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.