Coronavirus

Iyalan gidan sarautar Saudiya sun kamu da coronavirus

Sarki Salman Salman bin Abdulaziz na Saudiya ya kebe kansa a wani tsibiri  don gudun kamuwa da coronavirus
Sarki Salman Salman bin Abdulaziz na Saudiya ya kebe kansa a wani tsibiri don gudun kamuwa da coronavirus Bandar Al-Jaloud/Saudi Royal Palace/AFP

A kalla iyalan gidan Masarautar Saudiya 150 sun kamu da cutar coronavirus da suka hada da gwamnan birnin Riyadh wanda yanzu haka ke kwance a sashen kula da marasa lafiyar da ke cikin matsanancin hali a asibiti, kamar yadda Jaridar New York Times ta Amurka ta rawaito.

Talla

Likitocin da ke kula da iyalan gidan sarautar sun samu takardar umarnin ware gadaje a kalla 500 a asibitin Sarki Faisal saboda yiwuwar samun karin mutane daga gidan sarautar dauke da cutar.

Masarautar Saudiyar ta bai wa asibitin umarnin fitar da duk wani mara lafiyar da ke cikin matsanancin hali domin tanadar gadaje ga iyalan masarautar a cewar Jaridar New York Times.

Rahotanni sun ce, yanzu haka Sarki Salman mai shekaru 84 ya kebe kansa a can wata fadarsa da ke kan tsibirin tekun Maliya a kusa da birnin Jeddah , yayin da Yarima Mai Jiran Gado, Mohammed bin Salman ya kwashi ministocinsa don komawa wani sashi na tsibirin, inda ya yi alkawarin gina sabon birni mai suna Neom.

Coronavirus ta kashe mutane 41 a Saudiya tun bayan bullarta fiye da makwanni shida a kasar, yayin da aka tabbatar cewa, mutane dubu 2 da 795 na dauke da annobar a yanzu haka.

Ministan Lafiyar Saudiya, Tawfiq al-Rabiah ya gargadi cewa, nan da ‘yan makwanni masu zuwa, za a iya samun mutane kimanin dubu 200 dauke da cutar coronavirus a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.