Coronavirus

Mutun-mutumin da ke yaki da coronavirus

Ana amfani da mutun-mutumi wajen aiwatar da ayyukan da suka gagari bil'adama ko kuma ke da matukar wahala ga dan Adam
Ana amfani da mutun-mutumi wajen aiwatar da ayyukan da suka gagari bil'adama ko kuma ke da matukar wahala ga dan Adam Space

Kamfanin Forth Engineering da ke lardin Cumbria a Birtaniya ya kera mutun-mutumin wato 'Robot' a turance da ke feshin kashe kwayoyin cutar coronavirus a cikin kankanin lokaci.

Talla

Darektan kamfanin, Mark Telford ya ce, mutun-mutumi na da kayatarwa, inda a cikin minti 20, ya feshe wuri mai fadin murabba’i dubu 68.

Darektan ya ce, mutun-mutumin na dauke da tulun ruwa da kyamarar daukar hoto har ma da wuta.

A  cewar darektan, yanzu haka, an yi odar wani adadi mai yawa na wannan mutun-mutumin.

Ana iya sarrafa mutun-mutumin daga nesa, inda ake  ba shi umarnin tsaftace wurare a daidai wannan lokaci da ake fama da annobar coronavirus.

Asibitoci da ma’aikatau da shaguna duk za su iya amfani da wannan fasashar wajen yaki da coronavirus a cewar kamfanin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.