Lafiya

Sama da yara miliyan 100 na fuskantar barazanar Kyanda

Cutar Kyanda na barazanar yi wa yara miliyan 117 illla a sassan duniya
Cutar Kyanda na barazanar yi wa yara miliyan 117 illla a sassan duniya AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, kimanin yara miliyan 117 na cikin hadarin kamuwa da Kyanda a sassan duniya, la'akari da yadda gwamnatocin kasashe suka dakatar da riga-kafin cutar ta hanyar karkata hankalinsu wajen yaki da annobar COVID-19.

Talla

Sanarwar hadin guiwar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ta bayyana yadda hatta kasashe 24 da ke tsananin fama da cutar Kyandar, suka dakatar da riga-kafin cutar, yayin da suka tattara karfinsu a yaki da coronavirus.

Cikin sanarwar, hukumomin lafiyar sun bayyana cewa, wajibi ne kowacce kasa ta dauki matakan yaki da annobar coronavirus, sai dai hakan ba ya nufin a yi watsi da lafiyar miliyoyin kananan yara da ke bukatar agajin duniya.

Cutar Kyanda wadda a kowacce shekara ta na kama yara miliyan 20 ko fiye da haka  a sassan duniya duk da araha da kuma wadatuwar maganinta, ta kashe yara dubu 140 galibinsu wadanda shekarunsu bai haura biyar da haihuwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.